Acts 17

A Tassalonika

1Da suka bi ta Amfifolis da Afolloniya, sai suka isa Tassalonika, inda akwai majamiʼar Yahudawa. 2Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majamiʼar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi, 3yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesun da nake sanar muku shi ne Kiristi.” 4Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Helenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.

5Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ʼyan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka ta da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron. 6Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ʼyanʼuwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa: “Waɗannan mutanen da suke ta da fitina koʼina a duniya sun iso nan, 7Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.” 8Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi. 9Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki saʼan nan suka sallame su.

A Bereya

10Da dare ya yi, sai ʼyanʼuwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majamiʼar Yahudawa. 11Bereyawa kuwa sun fi Tassalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne. 12Yahudawa da yawa suka gaskata, haka ma waɗansu manyan matan Helenawa da kuma mazan Helenawa da yawa.

13Da Yahudawan da suke a Tassalonika suka ji cewa Bulus yana waʼazin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma ta da hankalinsu. 14Nan da nan ʼyanʼuwa suka sa Bulus yǎ tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya. 15Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens saʼan nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.

A Atens

16Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka. 17Saboda haka ya yi ta muhawwara a majamiʼa da Yahudawa da kuma Helenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa. 18Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana waʼazin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana waʼazin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu. 19Sai suka ɗauke shi suka kawo shi wurin taron Areyofagus, inda suka ce masa, “Ko za mu san mene ne sabon koyarwan nan ya kunsa da kake yi? 20Kana kawo mana raʼayoyin da suke baƙo a gare mu, kuma muna so mu san mene ne suke nufi.” 21(Duk Atenawa da baƙin da suke zama a can suna zaman kashe wando ne kawai kuma ba abin da suke yi sai dai taɗi da kuma jin sababbin raʼayoyi.)

22Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce: “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai. 23Gama saʼad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu: ‘GA ALLAHN DA BA A SANI BA.’ To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.

24“Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace alʼummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokatai bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’

29“Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse-siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. 30A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a koʼina su tuba. 31Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shariʼa da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin ta da shi daga matattu.”

32Saʼad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jinka a kan wannan batu.” 33Da wannan, Bulus ya bar Majalisar. 34Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.

Copyright information for HauSRK